Me askin da yafi kowani me Aski daɗewa a duniya


Aka ce inda ranka kasha kallo dan kuwa hotunan wani dattijo ne suke ta kareɗe shafukan sada zumunta, Inda aka ayyana shi a matsayin mai askin da yafi kowani me Aski daɗewa wa A DUNIYA. Wannan ba abinda mamaki bane ga wanda ya karanta cikakken labarin wannan mai askin. 

Biyo mu cikin wannan Rubutun domin karanta labarin wannan mai askin. 
Shidai wannan mutumin wanda dan asalin Kasar Amurka ne ya sha lashe kyaututukka saboda bajintar shi da kuma ke tare iyakokin da ba'a taba samu ba ko da a labarin almara. 

An tabbatar da cewa yafi sama da shekara 97 yana wannan sana'a, haka ne ya zamo na farko a cikin mutanen da suka fi kowa daɗewa suna sana'ar su, shidai wannan bawan Allah ya fara sanar ne tun yana shekara goma a duniya. 

Yawanci mun sani cewar mutane da yawa suna dena wani aiki ne da zarar sun kai shekaru 70 zuwa sama (lokacin tsufa), amma abin mamaki yadda wannan bawan Allah ya shafe kusan shekaru dari yana sana'a daya. 

Wannan me Aski ya kware inda yake samun kostomomi daga koina a fadin duniya inda yan jarida suna yawan zuwa hira dashi, an sha tambayar shi menene sirrin wannan shekaru nashi, amsar shi daya ce shi ne shi ma Be sani ba, yace da yana da wani sirri da ya bawa matar shi wadda ya mutu da dade wa, yace yana mutukar kewarta, yace babban kostoman shi shi ne Ɗanshi me shekaru sama da 89 a duniya. 

Post a Comment

0 Comments