"Ƴaƴa 11 na haifa a duniya kuma dukansu makafi ne" cewar Agnes mahaifiyar waɗansu makafi masu bara


Wani faifan bidiyo mai ban tausayi da matuƙar sosai zuciya ya ɓulla a social media  Inda mutane da dama suƙe ta tofa albarkacin bakunan su. 


Bidiyon dai, na wata mata ce wadda yake kira Agnes tayi kaurin suna a yankin da take, a Kasar Cameroon, musamman wajen yadda take bara ita da ƴaƴanta makafi su 11 reras.


A hira da akai da wannan baiwar Allah, malama Agnes ta fara bayar da tahirin cewar tayi aure cikin lumana ga miji na kwarai, kuma suna zaman lafiya har suka haifi dansu na farko, seda aka daɗe da haifar ɗan sannan suka gane baya gani, suka kai shi asibiti likita ya tabbatar musu cewa  dama chan baya haife shi yana gani ba, ma'ana dama a makaho aka haife shi, ba a iya nan abun ya tsaya ba domin kuwa ɗansu na biyu ma baya gani, haka zalika na uku, na hudu har zuwa na goma sha ɗaya, daga nan mutanen kauyen suka fara tuhuma Agnes da maita, wasu kuma su ce ta nemi temako daga wajen Mayu lokacin tana da ciki, amma duka wannan Be  tayar mata da hankali ba, hai seda aka wani gari mijin ta ta mutu, daga nan sabon shafi ya buɗe wa Agnes a rayuwa domin kuwa bata iya ciyar da duka yayansu, wanda wannan ne dalilin da yasa ya fara bara ita da Yayan nata, tace bata da kudin kaisu makaranta shiyasa basu taba shiga aji ba. 

Post a Comment

0 Comments