Ba zan sauka ba har se an biya ni kudi na.


Yadda wani magidanci ya tada hayaniya a banki, bayan sun cire mai naira miliyan 17 ba tare da ya sani ba, a daya daga cikin ban manyan baku nan Najeriya. 

A sadiyat yau ne wannan bidiyo ya billa wanda jaridar instablog ce ta fara wallafa shi a shafinta na Instagram, bidiyon ya dauki hakulan Ma'abota shafukan sada zumunta inda suke ta sharhi akan bidiyon. 


A cikin bidiyon za'a ga yadda wannan magidanci hakurin shi ya kare, inda ya tuɓe riga yana ta sunbatu bayan an cire mai naira miliyan 17 daga asusun shi batare da ya sani ba, wata me amfani da Shafin Instagram ta bayyana cewa Itafa bata ga laifin shi ba a yadda Kasar nan take duk wanda ya samu miliyan 17 ta hanyar halali to baze yarda a salwantar mai da kudi a banza ba. 

Post a Comment

0 Comments