Kazanta ko talauci: Bidiyon Matashin da yake dangwala ruwan kwata da burodi


Biyo bayan hauhawar masu amfani da shafukan sada zumunta, musamman TikTok mutane da yawa masu amfani da waɗannan shafuka sukan yi abubuwa da dama wajen, neman suna kama daga zagi, rawa, ko batsa da makamantansu. 


A yau wani bidiyo mara dadin kallo ya ɓulla a shafukan sada zumunta, Inda aka ga wani matashi riƙe da sinƙin burodi a hannu, zaune a gefen wani ruwan tabo yana gutsuro burodin yana dangwalawa da ruwan yana ci. 


Bidiyon yayi mutuƙar daukar hankalin masu amfani da, shafukan sada zumunta inda yawancin masu sharhi akan abun sun bayyana da cewar wannan Sede hauka don talaucin ƙasar be kai wannan mataki ba. 

Shin menene ra'ayin ku dan gane da wannan matashi, aje mana a akwatin komen dinka. 

Post a Comment

0 Comments