Wata budurwa ta cire tsoro ta fito ta bayyana abinda ya faru da ita da tsohon mijin ta, Alal hakika mun san cewa akwai malamai daga bangaren addinai da dama da suke amfani da addini wajen biyan bukatun kansu, wadanda ake kira malamai masu ci da addini.
Bidiyon wata mata wadda ta bayyana cewar a yanzu shekarunta basu wuce 22 zuwa 23 ba, tace tayi aure tana da shekaru 15 ta auri faston Cocin da take halarta, tace a lokacin bata san menene aure bama ta haifi ɗan ta na farko tana da shekaru 17 na biyu tana da shekaru 19,ta bayyana yadda rana daya mijin nata yazo ya faɗa mata Yesu yayi mai wahayi ya sake ta, ya kuma bayyana cewar Yesu yace ya auri budurwar shi da suke soyayya da ita.
0 Comments