Tsohon ɗan dambe a Amerika ya musulunta, yayi sallah karo na farko.Tsohon dan dambe wato Tate Andrew  ya karbi addinin Musulunci, inda yayi sallah karo na farko acikin wani gajeren bidiyo. 

Tate Andrew wanda shahararren dan dambe ne wanda aka haifa A Chicago, ya girma a Luton, tsohon ɗan wasan ya taba bayyanawa cewa musulunci shi ne addinin karshe wanda yake gaskiya. 

Labarin musuluntar dan wasan ya fara ne Lokacin da ya wallafa wani saƙo a shafinshi na sada zumunta, ya ce" wannan dalilin ne yasa neke musulmi, ko wani kirista da ya yarda da abu me kyau kuma ya yake fahimtar gaskiyar yaƙi akan abu mara kyau, to tabbas ya musulunta" sannan Tate ya kawo aya a cikin Alkur'ani, to musuluntar shi bata tabbata ba seda aka ganshi a cikin masallaci yana sallah a wani guntun bidiyo. 

Post a Comment

0 Comments