Yadda aka samo wani mutum wanda ya ɓata a Ramin ɓera.


Mutumin dan shekaru 64 me suna aya osei, wanda ake ta nema bayan ɓacewar shi kusan har kusan kwana uku ana nema, a kauyen Sehwi Asempanaye dake kudancin Kasar gana, an gano shi a cikin daji. 

Mutumin de a yadda muka samu labari ya bar gida ne domin zuwa gona yayi noma, to anan ne ya haɗu da dabbar inda a ƙoƙarin kama ta ne hannun shi na dama ya maƙale a cikin Ramin ɓeran har na tsawon kwana uku. 


Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane su biyu suka gano dattijon, a cikin daji lokacin da suka je Yo itace, anan suka tarar da shi ja jigata kamar wanda ba rai, inda take-yanke suka gayyato jama'ar wannan gari domin su shaida wa idanun su. 


Dattijawan wannan gari sun bayyana mutuwar mamakinsu ga faruwar wannan al'amari inda suka bayyana dole su zage damshe wajen kare ganin nasu da tsafi domin gujewa shigowar sheɗanu garin nasu. 

An tono mutumin daga ramin, inda aka ce har kan shi ma ya maƙale a jikin jijiyar bishiyar, kuma jikin shi ya jiƙe da taɓa. Post a Comment

0 Comments