Allahu Akbar yadda wata yarinya ta jawo hankulan Ma'abota shafukan sada zumunta bayan an bayyana ta cewar ta haddace Alkur'ani kaf a cikin wata huɗu.
Babban abinda ya fi ko wanne ban mamaki shi ne yadda yarinyar take da karancin shekaru, duk da akwai wadanda suka tafi kan cewar kwakwalwar yara tafi ta manya sauki daukar abu, amma hadda Alkur'ani tasha bambam da wasu abubuwa saboda dole seka karanta ka kara karantawa, kullum kamar yadda malamai suke faɗa "ita hadda Alkur'ani rakumi ce da Akala inde baka dinga daure shi ba to lallai wata rana zaka nemi shi ka rasa"
0 Comments