Yadda budurwa ta zane mahaifiyarta bayan fasto ya faɗa mata mayya ce.


Wannan duniyar dame tayi kama, yau wani bidiyo ya dauki hankulan masu amfani da shafuka sada zumunta inda wata budurwa take jibgar mahaifiyarta da bulala bayan fasto ya faɗa mata mahaifiyarta wai mayya ce. 

Amfani da shafukan sada zumunta ya bayar da gudummawa wajen tona asirin maluman addini iri-iri na karya, waɗanda suke amfani da addini wajen dulmiyar da magoya bayan su. 

A safiyar yau ne wani bidiyo ya billa inde aka ga wata budurwa wadda bata fi shekara 25 zuwa 30 ba, tana lakaɗawa mahaifiyarta uban dukan inda take cewa mahaifiyarta ta bayyanawa mutanen gari ita mayya ce, budurwar de wani fasto ne yace bata samun cigaba ne saboda mahaifiyarta mayya ce, bayan ta dawo gida ya samo bulala Inda take ta jibgar mahaifiyarta. 

Post a Comment

0 Comments