Yan sanda sun damƙe malamar da take siyowa dalibai abinci da kuɗin albashin ta.


A kace inda ranka ka sha kallo, a yau muke samun labarin wani abu da ya faru a kasar Ghana inda wata malamar firamare, ta shiga hannun jami'an tsaro bayan bullar bidiyonta tana ciyar da Yaran makarantar abinci me rai da lafiya kyauta, daga cikin kudin Albashin ta. 


Malamar me suna Abena sarwaah mankosa, ta dauki hankulan mutane da dama tun biyo bayan bullar hotunan ta, tana ci yar da Yaran kyauta yan kwanaki kaɗan da suka wuce. 


Jim kadan biyo bayan haka Hukumar ilimi ta gana ta bayyana, Abinda malamar tai a matsayin karya dokar aiki, kuma abinda baza su juri suga ana aikatawa ba. Malamar ta bayyana cewar Hukumar ta gayyace ta domin ta bada cikakken bayanin Meyasa take aikata irin wannan abun, kuma miye manufarta. 

Hukumar tana zargin malamar da aikata haka ne domin ta dinga samun temako daga masu kudi da hannu da shuni da kuma neman suna. 

Post a Comment

0 Comments