Wani bidiyo da ake ta yaɗawa, ya dauki hankulan mutane da yawa, inda kusan sati biyu har yau suna tofa albarkacin bakunan su, a cikin bidiyon wata mata ce take bayani yadda ta haifi yarta ta farko amma cikin Ikon Allah se yar ta zo bata gani.
Matar me suna karie shanee, wadda alamu sun nuna, ta fito ne daga Kasar Amerika ta wallafa wani guntun Bidiyo a shafinta na TikTok, inda karo na farko a faɗar ta zata nunawa duniya diyarta wadda bata gani ba tare da taji kunya ba.
Karie ta bayyana cewar da farko bata taba tunanin zata haifi yarta a makance ba, amma kash se hakan ya faru tace tun kafin ta haihu ta fara shiryawa yar tata, yadda zata more rayuwar ta da kudin makaranta, "mutane da yawa suna ta magana akai to amma ni bani jin kunyar nunata tunda Allah ne ya bani ita" cewar karie shanee
0 Comments