Wani yaro dan shekaru 8 ya kashe maciji har lahira da cizo.




A yau ne muke samun labarin wani abu da ya faru achan Raipur dake Kasar Indiya inda wani abun ban al'ajabi ya faru tsakanin wani karamin yaro dan shekaru 8 da wani jibgegen maciji. 


Kamar yadda waɗanda abun ya faru akan idon su, macijin a ciji Yaron ne sannan kuma ya kanannaɗe a jikin hannun Yaron, inda yayi yayi da jefar da macijin amma ya kasa, shi ne dalilin da yasa Yaron yaga ba wani mafuta kawai ya gantsarawa macijin ciro. 



Take a ka Lauki Yaron zuwa asibiti likitan da yake kula da cizon maciji ya dan bashi wasu yan magunguna, sannan ya sallame shi, likitan yayi bayani cewar hatta cizon da macijin yayi wa yaron, ba wani cizo bane me cutar wani. 


Dagacin kauyen ya shedawa manema Labarai cewa a tarihin kauyen, haka bata taɓa faruwa ba, ya bayyana cewar kauyen nasu Allah ya hore musu yawan macizai. 

Post a Comment

0 Comments