Yadda wani magidanci ya fille kan matarshi bayan ta bude mai waya Be sani ba.


Hausafeed ta samu labarin yadda wani magidanci dan shekaru 40 ya fille kan matarshi yar shekaru 38 a chan gaba shin Afirika. 


A bayanan da yan sanda suka nuna sun tabbatar da faruwa al'amari, inda suka bayyana cewar mutumin, sunyi aure da matar ne wata biyu da suka wuce inda tun bayan auren su basa zama lafiya. 


A sati daya kafin faruwar lamarin matar shi ta daukar mai wayarshi ta yi mai bincike ba tare da saninshi ba, wanda bayan da lura da abin da ya faru ya jawo, faɗa me tsananin su, daga karshe ya nemi wata yar uwarshi yace ta sasanta shi da matar tashi. 

Kwatsam rana daya ya tashi ya dauki adda inda ya sassari matar tashi har seda ta mutu, ya nufi wajen mahaifiyarsa yace ta kula mai da yayanshi, ita kuma mahaifiyar se zargi ya kamata ta nufi gidan shi take taga abinda ya faru. 

Post a Comment

0 Comments